ABNA24 : Bayanin ya ce an kammala kidayar fiye da kashi 90% na dukkanin kuri’un da aka kada, kuma Ibrahim Ra'isi ne ya bai wa sauran ‘yan takarar tazara mai nisa, wadda ke tabbatar masa da lashe zaben.
Bayanin ya ce mutane miliyan 28 da dubu 600 ne suka kada kuri’unsu, daga mutane kimanin miliyan 60 da suka cancanci kada kuyri’a a kasar, inda Ibrahim Ra’isi ya zuwa ya samu kuri’u miliyan 17 da dubu 800, sai kuma Mohsen Reza’i milyan 3 da dubu 300, Abdlnasir Himmati miliyan 2 da dubu 400, sai Amirka Hussain Qadi Zade Hashemi kimanin kuri’u miliyan 1.
A yau ne ake sa ran za a kammala sanar cikakken sakamakon a hukumance.
Shugaba Rouhani ya mika sakon taya murna ga Ibrahim Ra’isi dangane da wanann nasara da ya samu, kamar yadda dukkanin sauran ‘yan takarar sun mika sakonninsu an taya shi murna dangane da nasarar lashe zaben